- Yayin da ake shirin shiga zanga-zanga a Najeriya, kungiyar matasa ta tura bukatunta ga gwamnan jihar Ogun a rubuce
- Kungiyar Take it Back Movement (TIB) a jihar ta bukaci Gwamna Dapo Abiodun ya samar da tsaro da kuma bas bas ga matasan
- Kungiyar ta kuma bukaci ya gargadi duka masu yi musu barazana a jihar musamman kungiyoyin direbobi da 'yan tasha
Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru uku.
Jihar Ogun - Kungiyar Take it Back Movement (TIB) reshen jihar Ogun ta shirya komai domin fita zanga-zanga a gobe Alhamis 1 ga watan Agustan 2024.
Kungiyar ta bayyana wasu wurare da za a hadu musamman kafin fara zanga-zangar yayin da ake cikin wani mummunan yanayi.
Awanni kafin fita tituna, APC a Kano ta roki matasa alfarma kan lamarin zanga zanga
Zanga-zanga: Matasa sun shirya fita a Ogun
Shugaban tawagar a jihar, Festus Akanbi Afofun shi ya bayyana haka a cikin wata wasika ga gwamnatin jihar, cewar Daily Trust.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Afofun ya bukaci gwamnatin jihar ta ba su dukkan kariya yayin da za su fara daga 1 zuwa 10 ga watan Agustan 2024, Sahara Reporters ta tattaro.
Kungiyar ta kuma bukaci motacin bas daga gwamnatin jihar domin taimaka musu inda ya ce rashin yin hakan zai iya jawo matsala.
Bukatar kungiyar zanga-zanga zuwa gwamna
"Ina mai sanar da kai cewa ya rataya a wuyanka ka samar da tsaro ga dukkan masu zanga-zanga da kuma kula da su.""Mai girma gwamna, muna bukatar ka yi amfani da girman ofishinka domin ba da kariya da dukkan abin da ake bukata.""Daga ciki akwai samar da bas bas domin daukar masu zanga-zanga da kuma dawo da su daga safe zuwa yamma har zuwa karshe."Saura kiris a fara zanga zanga, gwamnan Yobe ya sa labule da shugabannin hukumomin tsaro
- Festus Akanbi Afofun
Matasa sun zargi wasu miyagu kan zanga-zanga
Afofun ya ce suna sane da shirin wasu miyagu domin kawo tsaiko a lamarin zanga-zangar a fadin jihar baki daya.
Ya bukaci gwamnan da ya yi gargadi ga kungiyoyin sufuri da 'yan tasha game da kai farmaki kansu kamar yadda suke barazana.
Matasa sun fasa motar abinci a Cross River
Kun ji cewa wasu matasa sun farmaki babbar motar bas makare da kayan abinci a jihar Cross River inda suka raunata da dama.
Motar dauke da kayan abinci a cike ta nufi sakatariyar kungiyar 'yan jaridu ne a jihar domin rabon tallafi ga mambobinsu.
Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.
Asali: Legit.ng
ncG1vNJzZmigkarAonrLnp6irF6jtHC6xLCqaGlmZYJ1fJRmopplo5a6or6MppinmV2Zrm65zq2mnKGeYq%2Biv4ymmKytXa%2Bur7PAZrGappeWerTBzWarrqqRYq%2B2t8CtrKerpWK0onnGsJimppFk